Koroma ya ki yarda da dokar zubar da ciki

Hakkin mallakar hoto AP

Shugaban kasar Saliyo Ernest Bai Koroma ya sake kin amincewa ya sanya hannu a kan kudirin dokar halasta zubar da ciki wadda daukacin 'yan majaliar dokokin kasar suka zartar a watan Disamba.

A yanzu dai Mr Koroma ya mika daftarin ga kwamtin nazarin kundin tsarin mulki.

Duk wani gyara da kwamitin ya bada shawara za a gabatar da shi ga 'yan kasa domin kada kuri'ar raba gardama.

A yanzu dai zubar da ciki ko ta wane hali haramun ne a kasar Saliyo.

Shugabannin addini sun yi korafi a kan sauya dokar yayinda a waje guda kuma masu rajin bada zabi ga jama'a ke cewa halasta zubar da ciki zai rage yawaitar mace macen mata a hannun likitocin da basu kware ba.