Turkiya ta kai hari kan 'yan PKK a Iraqi

Hakkin mallakar hoto AFP getty Images

Rundunar sojin Turkiya ta ce ta kashe yan tawayen Kurdawa 67 a wani farmakin sama da ta kai a cikin wannan makon a sansanoni da cibiyoyin adana makamai na haramtacciyar kungiyar PKK a arewacin Iraqi.

Wata sanarwa ta sojin ta ce an kar hare haren ne a ranar Laraba.

Hari makamancin wannan da aka kai a kan sansanonin PKK shine wanda aka kai a watan da ya gabata bayan wani harin kunar bakin wake a Ankara wanda ya hallaka mutane 29.

Tun bayan rushewar yarjejeniyar tsagaita wuta a watan Yuli ake samun karuwar arangama tsakanin jami'an tsaron Turkiya da yan tawayen Kurdawa