Fina-Finai kan matsalolin mata a duniya

Image caption Fina-finan sun kun shi bayanan matsalolin da suke shafar akasarin mata a kusurwoyin duniya.

Wata gidauniyar kasar Faransa mai suna ELLE, ta tattara wa su gajejjerun fina-finai goma sha daya na tsawon minti daya da rabi ko wanne da aka watsa a gidajen talbijin na kamfanin France Televisions.

Wadannan fina-finai sun kun shi bayanan matsalolin da suke shafar akasarin mata a kusurwoyin duniya.

Matsalolin sun hada da talauci da kuma barazana ga rayuwar matan, koda yake, matan su na kokari don shawon kan matsalolin da suka fada a ciki.

Daukacin matan dai sun fito ne daga kasashe masu tasowa, kuma daya daga cikin wadannan matan ita ce Hawa'ou Adamou Shugabar kungiyar AFHADEV dake tallafa wa mata.

A hira da BBC, Shugabar kungiyar ta AFHADEV ta ce tana yunkurin ganin sun samu mallakar abin kan su domin su taimaka wa mazajensu na aure.