An kai hari wurin shakatawa a Ivory Coast

Hakkin mallakar hoto Reuters

Yan bindiga sun kai hari wani otel a wurin shakatawa na gabar kogi na Grand Bassam a kasar Ivory Coast

Rahotannin sun ce an sami jikkatar jama'a.

Wadanda suka shaidar da lamarin sun ce maharan wadanda ba a san ko su wanene ba, sun bude wuta a kan baki masu shakatawa.

Wani hoton da aka sanya a yanar gizo ya nuna mutane su na tserewa daga bakin kogin.

Wurin shakatawar na Grand Bassam da ke tazarar kilomita 40 daga gabashin Abidjan babban birnin kasar shi ne wurin shakatawa mafi shahara da daukar hankalin yan yawon bude ido.

Ana dai daukar kasar Ivory Coast a matsayin zakaran gwajin dafi wajen zaman lafiya da kwanciyar hankali kafin a sami barkewar rikici tsakanin arewaci da kudancin kasar a shekarar 2002.