Yadda karfin batirin wayar Apple ya ke

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Wasu ma su wayar Apple ba sa rufe manhajar da suka bude inda suke zaton yin hakan na kara karfin batirin iPhone

Kamfanin Apple ya tabbatar cewa kunna manhaja a bar shi a bude a wayar iPhone baya shafar karfin batirin wayar.

Kamfanin ya bayyana haka ne bayan wani mutum da ke amfani da wayar ya aike da sakon Email ga shugaban kamfanin inda yake neman karin bayani game da kunna manhaja a wayar Apple.

Mutumin mai suna Caleb dake zaune a Ohio a sakon da ya aike wa Tim Cook da sako inda ya yi tambaya kan ko rufe manhajoji na kara karfin batirin wayar ?

Mataimakin shugaban kamfanin Craig Federighi ya mayar masa da amsar cewa ko kadan ba haka ya ke ba.

Koda ya ke batirin sauran wayoyin tafi da gidan ka su kan kara karfi idan aka rufe wa su manhajoji da aka bude a wayoyin.

Wasu ma su amfani da wayar Apple dai ba sa rufe manhajar da suka bude a wayar inda suka yi amannar cewa yin hakan na kara karfin batirin na iPhone, koda yake wannan ba shawara ce da kamfani ya ba masu amfani da wayar ba.