Ana duba lafiyar jiragen sama na Nigeria

Hukumar kula da lafiyar jiragen sama ta kasa da kasa wato (ICAO), ta fara duba koshin lafiyar jiragen sama na Nigeria.

Binciken dai na zuwa bayan shekaru 10.

Rabon da hukumar ta ICAO ta gudanar da irin wannan bincike dai tun a shekara ta 2006.

Wakilinmu na Legas Umar Shehu Elleman ya zanta da manajan daraktan hukumar kula da koshin lafiyar jiragen sama a Najeriya, Captain Mukhtar Usman, a game da zuwan hukumar ta ICAO kasar.

Na'urarku na da matsalar sauraren sauti

A baya dai an sha samun hadarin jiragen sama a Najeriya wanda masana ke cewa rashin kulawa da jiragen ne.