Ivory Coast: Za a gudanar da taro kan ta'addanci

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Mutane 16 ne suka mutu sakamakon harin

Shugaban kasar Ivory Coast Alassane Ouattara, zai gudanar da taron gaggawa a ranar Litinin, domin tattaunawa a kan harin da masu da'awar jihadi suka kai bakin teku.

'Yan bindigar sun kashe mutane 16 da suka hada da sojoji a otal din Grand Bassam kusa da birnin Abidjan.

Wata mata ta ce ta yi tsammanin 'yan bindigar jami'an tsaro ne amma sai ta ga sun bude wa masu yawon bude ido da ke bakin tekun wuta.

A karshe dai jami'an tsaro sun shawo kan lamarin.

Kungiyar Al-Qaeda ta dauki alkahin kai hari.

Wannan hari dai ya biyo bayan hare-haren da aka kai wasu otal-otal a kasashen Mali da Burkina Faso.