Birtaniya za ta hana tallar kwalam a intanet

Hakkin mallakar hoto ThinkStock
Image caption kayan kwalam

Hukumar da ke sa ido a kan tallace-tallace ta Birtaniya ta ce nan ba da dadewa ba za ta haramta tallar kayan kwalam ta intanet.

Tuni dai aka haramta tallar kayan abincin kananan yara ta talabijin, wanda ake ganin yana da hadari ga lafiyarsu.

Nan ba dadewa ba ne kwamitin da ke kula da tallace-tallace, wanda ya tsara wa masu talla wadansu ka'idoji zai fara tuntubar jama'a a kan wannan batu.

Haramta tallace-tallacen za ta shafi dandalin YouTube da ITV Hub.

A shekara ta 2007 ne hukumar da ke sa ido a kan gidajen radiyo da talabijin ta fiatr da wasu tsauraran sharuda, wadanda suka haramta tallar kayan kwalam ko abinci mai yawan kitse da sukari da kuma gishiri, musamman ma a cikin shirye-shiryen gidajen talabijin, wadanda suka shafi yara 'yan kasa da shekara 16.