Musulman Liberia sun koka kan tsarin addini

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Shugabar kasar Liberiya Ellen Johnson Sirleaf

Wata sabuwar kwaskwarima da aka yi a kan kundin tsarin mulkin kasar Liberia, ta bayar da shawarar cewa, a dauki addinin Kirista a matsayin addinin da al'umma kasar ke bi.

Wannan matakin da bai yi wa al'ummar Musulmin kasar dadi ba.

A wani mataki na nuna kin amince wa da hakan, a yanzu al'ummar Musulmai sun janye daga majalisar addinan kasar, wata majalisa mai karfin fada a ji ta fuskar samar da jituwa a tsakanin manyan addinan biyu.

A baya dai ana kallon kasar Liberia a matsayin kasar da ba ruwanta da addini, to amma a yanzu tilas sai mutanen kasar sun yi muhawara da nuna amince wa kafin wannan kuduri ya zama doka.

Akasarin al'ummar Liberia dai Kiristoci ne, koda yake akwai Musulmai da kididdiga ta nuna sun kai kashi 15 zuwa 20 cikin 100 na al'ummar kasar.