A sauyawa 'yan ta'adda Suna: Erdogan

Reccep Tayyip Erdogan Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Turkiyya na fama da hare-haren ta'addanci.

Shugaban Turkiyya, Reccip Tayyip Erdogan ya ce ya kamata a sake nazari don sauya ma'anar ta'addanci ta yadda za ta hada da duk wanda ya taimaka wajen aikatawa, ciki har da 'yan jarida da 'yan majalisar dokoki.

Yana jawabi ne kwana guda bayan wani harin kunar-bakin-waken da ya halaka mutum 34 a Ankara.

Babu dai wanda ya dauki alhakin kai harin, amma gwamnatin Turkiyya ta ce babu tantama, kungiyar 'yan tawayen PKK ce ta kai harin.

Sojojin Turkiyya dai na ci gaba da kai hare-hare a a kan mayakan PKK da ke birane da dama da ke kudu-maso-gabashin kasar tun lokacin da wata yarjejeniyar dakatar da bude-wuta ta wargaje bara.