Google: A daidaita dokar mota marar matuki

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Motar Goole marar matuki

Shugaban sashen da ke kera mota marar matuki na kamfanin Google, Chris Urmson ya bukaci 'yan majalisar dokokin Amurka daidaita dokokin da suka shafi fasaha a kasar.

Chris Urmson ya shaida wa majalisar dattawan Amurka cewa ya kama a ba wa Sakataren sufurin Amurka iko a kan al'amuran da suka shafi dokokin maimakon a kyale kowace jiha tana yin nata dokokin a gefe.

Ya za a fi samu tsaro da kariya idan Fasinjoji ba sa yi wa motocin da ba su da matukan hawan-kawara.

Wannan matsayin nasa dai ya sha bambam da na mahukunta a Calofornia, wadanda ke goyon bayan cewa ya kamata a samu mutum da zai dinga lura da mota marar matukin.

Chris Urmson ya ce kawo yanzu jihohi 23 sun kafa dokoki 53 da suka jibinci mota marar matuki, kuma wasu daga cikin dokokin suna karo da juna, yana gargadin cewa za a kai matsayin da dokokin ba za su yi aiki a zahiri ba.