Shin ko Nigeria za ta iya farfado da masana'antunta?

Image caption Masa'antu da dama sun durkushe a Najeriya

A yayin da Najeriya ke kara shiga wani hali na matsanancin rashin aikin yi da kuma tabarbarewar tattalin arzikin inda ta dogara a kan man fetur, kasar na kokarin sauya hanyoyin da za ta dogara da su domin bunkasa tattalin arzikinta ta hanyar fara wani kamfe mai taken "amfani da kayayyakin da ake yi a Najeriya."

Wakilin BBC Martin Patience, ya je jihar Kano da ke arewacin kasar, domin gano rin gudunmuwar da za ta iya bayarwa ga wannan nufi.

Martin ya ce, "A lokacin da naje kamfanin yin tufafi na Gaskiya Textile, ba abin da nake gani sai yanar gizo-gizo ta ko'ina da kuma kura wajen dai ya zama tamkar kufai tun bayan rufe kamfanin a shekarar 2005."

A da Kano na daga cikin manyan cibiyoyin kasuwanci na Afirka. An san shaharar da birnin Kano ya yi wajen jawo hankalin 'yan kasuwa daga yankunan Sahara.

Amma a shekarun baya-bayan nan, al'amarin ya sauya ta inda kasuwancin ke neman tabarbararewa.

Hakkin mallakar hoto
Image caption Ma'aikata sun rasa aiki saboda rufe masana'antu a Najeriya

Kamfanin Gaskiya ya dauki ma'aikata 5,000 wadanda suke yin tufafin gargajiya na Afrika da tufafin makaranta da na sojoji har zuwa lokacin da aka rufe shi.

A yayin da ake samun karuwar gasar kasuwanci daga kasar China da yawan fasa kauri da tsadar kayayyakin samar da abubuwa -- hakan ya tursasa masana'antu da dama sun rufe kuma dubun-dubatar ma'aikata sun rasa ayyukansu.

'Abubuwa na bukatar sauyi'

A wani bangare na kamfanin, jerin injinan saka ne sama da 100.

Girman filin da aka jibge su zai kai girman filin kwallo.

Wani tsohon ma'aikaci wanda ba ya son a ambato sunansa, ya zagaya da ni ginin kuma ya shaida min cewar, yanayin lalacewar abubuwa a kamfanin na matukar tayar masa hankali.

Ya ce "A lokacin da na ke aiki a nan, ina sa ran kasata za ta samu kyakkyawar makoma."

Ya kara da cewa, "A da ni ma'aikacin wannan kamfanin ne, ta hanyar aikin da na yi da wannan kamfanin na samu ilimi na kuma yi aure na hayayyafa."

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Najeriya ta dogara a kan danyen mai

Na tambaye shi ko yana ganin akwai yiwuwar 'ya'yansa za su yi aiki da wannan kamfanin nan gaba? Sai ya ce, "Akwai bukatar abubuwa su sauya sosai, addu'ar da muke yi kenan."

Muryoyinmu sai amsa kuwwa suke yi a ma'aikatar da a da karar injuna kan cika ta amma kuma a yanzu ba ka jin komai sai shiru.

Rufin kamfanin ya yaye kuma injinan sun fara tsatsa.

Lallacewar da ma'aikatar ta yi, alama ce ta yadda babban kamfanin ya fadi.

Najeriya a lambobi:
  • Yawan al'umma - miliyan 178 --- Yawan mutanen da ya fi ko wanne a Afrika.
  • Kasar da ta fi kowace fitar da mai kuma mai tattalin arziki mafi girma a Afrika.
  • Mai ne ke samar da kashi 90 cikin 100 na abubuwan da Najeriya ke fitarwa kuma ya ke samar da kusan kashi 75 cikin 100 na kudaden shigar kasar.
  • Shekarar 2014: Mai da kuma iskar gas da Najeriya ke fitarwa ya ragu da kashi 1.3 cikin 100, bayan raguwar da yayi da kaso 13 cikin 100 a shekarar 2013.
  • Kididdigan girman tattalin arzikin kasa : Dala 3,000 a shekarar 2013 a alkaluman da bankin duniya ya fitar.
Bayanai: Bankin duniya, da OPEC'In baka yi, bani wuri'

Tattalin arzikin Najeriya na tangal-tangal sakamakon faduwar farashin mai a duniya - kasar na fuskantar ci gaban bunkasar tattalin arziki mafi kankanta a sama da shekaru 10.

Amma a yayin da ake kyautata zaton lokaci ya kurewa masana'antar Gaskiya, ana san ran abubuwa za su gyaru kamfanin.

Gwamnatin Najeriya dai tana so ta farfado da masana'antun kasar a kokarinta na sauya hanyar samun kudaden shigarta wajen bunkasa tattalin arzikinta.

Gwamnatin kasar na kamfe na "kayayyakin da aka yi a Najeriya" domin tallafawa masa'anantu.

Daya daga cikin kamfanonin da za su ci moriyar wannan shirin shi ne Kamfanin Terytex - daya daga cikin kamfanonin sarrafa tufafi da ke aiki har yanzu a birnin.

'Masana'antar da ke bunkasa'

Kamfanin na yi tawul da zanuwan gado na asibitoci da otal-otal. Yana da ma'aikata 200.

Mohammed Sani Ahmed, shi ne manajan daraktan, kamar yana mamakin yadda kamfanin ya cigaba.

Ya shaida min cewar an kiran shi wurin wani taro, "Na yi zaton za tsige ni saboda rashin yin kokari," in ji shi

"Amma kuma sai aka yi ta yabo na. Mun zaci za a rufe wannan kamfanin a shekarar da ta gabata."

Image caption Masu rini na zargin 'yan China da kwace musu kasuwa

Kafa masana'anta a Nijeriya na tattare da kalubale. Terytex na kashe dala miliyan 500 a shekara domin zuba mai a janareto saboda rashin isashiyar wutar lantarki.

Kuma idan aka samar da abubuwan, kafin aka su kasuwa, suna yi tsada.

Kalubale na baya bayan nan da Ahmed ke fuskanta: Ba zai iya samun kudin waje ya sayi bangarorin injina daga Turai ba.

Hakkin mallakar hoto State House
Image caption Buhari ya ce gwamnatinsa za ta magance matsalar rashin aikin yi

A yayin da ya ke nuna godiya ga kokarin da gwamnati ke yi na farfado da masana'antu, ya na kokwanto a kan shirin.

"Muna da tarihin irin wadannan shirin sai dai samar da shi ya kan gagara. Ba ma tsoron 'yan China, amma su biya kudin haraji kamar yadda ya kamata, ta haka ne za mu iya gasa da su," in ji Ahmed.

Najeriya na matukar bukatar samar da ayyukan yi - kusan matasa miliyan biyu ne ke neman aiki duk shekara.

'Rashin aikin yi'

A jihar Kano da kyar zaka rasa matasa maza wadanda ba su da aikin yi ba.

Nuhu Ibrahim matashi ne, ya ce " Idan har ba wani ka sani a gwamnati ba ko wanda zai tallafa maka wajen kasuwanci da kuma karatu ba, rayuwar na matukar wahala."

Kuma wannan shi ne kalubalen da gwamnatin kasar ke fuskanta: Ko dai na gyara tattalin arzikinta ko na ci gaba da funskantar tashe-tashen hankula.

Kungiyar Boko Haram ta lalata yankuna da dama a arewacin Najeriya, wanda rashin aikin yi ya taimaka wajen hakan.

A da baya jihar Kano ta yi kaurin suna sai dai babu tabbas a kan makomarta.