Na'urarku na da matsalar sauraren sauti

'Yan gudun hijira za su koma gida — Majalisa

Hakkin mallakar hoto Nigeria Senate
Image caption 'Yan gudun hijira na son komawa garuruwan su idan an tabbatar da tsaro a cikin su.

Majalisar Dattawan Najeriya ta amince da a samar da naira biliyan 10, kwatankwacin dalar Amurka miliyan 50, don mayar da 'yan gudun hijira gidajensu.

Za a yi amfani da kudin ne dai don sake tsugunar da 'yan gudun hijirar da ke sansanoni a jihohin Adamawa da Borno da Yobe.

Majalisar ta ce tuni sojojin Najeriya suka 'yantar da galibin garuruwan da 'yan gudun hijirar suka bari, wadanda a da suke hannun mayakan kungiyar Boko Haram.

Ga karin bayanin da Sanata Muhammad Ali Ndume, da ya gabatar da kudurin a gaban majalisar ya shaidawa BBC: