Trump da Clinton za su san matsayinsu

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Masu kada kuri'a na zaben 'yan takara

An fara kada kuri'a a jihohin North Carolina, da Ohio da Florida da Illinois da kuma Missouri na Amurka, a zaben fidda gwani na masu son jam'iyyun Demokrat da Republican su tsayar da su takarar shugabancin kasar a zaben da ke tafe.

Jihar Florida ce tafi yawan wakilai da za su kada kuri'a a wannan zaben.

Attajirin nan da ke kan gaba a yawan kuri'u a jam'iyyar Republican, Donald Trump yana fatan ganin ya kakkabe sauran abokan hamayyar sa a jam'iyyar.

A yayin da ita ma Hillary Clinton ta jam'iyyar Demukrat, take zage damtse don ci gaba da shiga gaban Bernie Sanders na jam'iyyar.

Zaben zai nuna makomar 'yan takara musamman Marco Rubio na jihar Florida.