Trump da Hillary sun cinye zaben fitar da gwani

Mai neman takarar shugabancin Amurka a jam'iyyar Republican, Donald Trump ya sake lashe zaben fitar da gwanin da aka yi a jihohi muhimmai guda uku, ciki har Florida.

A jawabin da ya yi ga magoya bayansa, Mr Trump ya bayyana cewa lokaci ya yi da 'ya'yan jam'iyyar za su hada kansu, ya kara da yiwa dukkan mutanen da suka marasa masa baya godiya.

Abokin hamayyarsa, Sanata Marco Rubio, wanda dan jihar Florida ne da ya sha kaye a gida ya sanar da ficewarsa daga takarar.

Ita ma mai neman takara a karkashin jam'iyyar Democrat, Hillary Clinton ta samu nasara a jihohin Florida da Ohio da kuma North Carolina.

Sai dai abokin hamayyarta, Bernie Sanders ya ce har yanzu bai daddara ba, zai ci gaba da yin takara.