An kai hari wata kasuwa a Yemen

Hari a Yemen Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption 'Yan tawayen Houthi na yaki da gwamnatin Yemen.

Jami'an lafiya a Yemen sun ce fiye da fararen hula 40 ne suka rasa rayukansu a hare-hare ta sama da aka kai a wata kasuwa da ke gundumar Mustaba.

Tun da fari kungiyar likitoci ta Medicins Sans Frontieres ta ce daya daga cikin asibitocin ta ya cika da marasa lafiya wadanda suka jikkata.

Yankin da aka kai harin dai wuri ne da 'yan tawaye na kabilar Houthi ke da rinjaye.

'Yan Houthi dai na yaki da gwamnatin Yemen da kuma dakarun kawancen da Saudiyya ke jagoranta, wadanda su ke kai hare-hare ta sama kan 'yan tawayen.

Mai magana da yawun kawancen Saudiyya ya ce ya yi wuri su yi tsoka kan harin, amma dai su na gudanar da bincike.