Lula ya yi kome a fadar shugaban Brazil

Hakkin mallakar hoto EPA
Image caption Mr Lula da Silva ya musanta zargin cin hanci

Tsohon shugaban kasar Brazil, Luiz Inacio Lula da Silva, ya amince ya karbi mukami a gwamnatin shugaba Dilma Rousseff da zarge-zarge suka mata yawa.

Tsohon shugaban zai zama sabon shugaban ma'aikatan fadar gwamnatin kasar.

Mista Lula da Sylva, wanda Ms Dilma Rousseff ta karbi shugabancin kasar a hannun sa, ya kasance ana gudanar da bincike a kan sa, kan zargin hannu da yake da shi a babbar badakalar kudi a kamfanin mai na kasar Petrobras.

Masu shigar da kara sun ce ya amfana ta haramtacciyar hanya daga kamfanonin gine-gine da suke da tabon karbar hanci da rashawa.

Lula dai ya musanta zargin, inda ya ce suna da alaka da siyasa.