Mata uku 'yan Brunei sun kafa tarihi

Hakkin mallakar hoto RoyalBruneiAirlinesInstagram
Image caption Matan da suka ciri tuta

Matuka jirgin sama uku mata na kamfanin jirgin sama na Brunei, sun kafa tarihi a kamfanin inda suka tuka jirgin sama zuwa Saudiyya.

Matan uku sun tuka jirgi kirar Boeing 787 Dreamliner daga Brunei zuwa Jeddah.

Babbar mai tuka jirgin sama, Kyaftin Sharifah Czarena, ta samu taimakon Sariana Nordin da Dk Nadiah Pg Khashiem.

Kyaftin Czarena wacce ta samu horo a Biritaniya, a shekarar 2013 ta kasance mai tuka jirgi ta kamfanin Royal Brunei ta farko, da ta tuka jirgi daga filin jirgin saman Heathrow.

"A matsayi na na mace a Brunei, wannan gagarumin cigaba ne. Kuma ya nuna cewa matasa musamman mata za su iya cimma burinsu," in ji Czarena.