An gano asalin dan bindiga a Brussels

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption 'Yan sanda a Belgium na ci gaba da dakile hare-haren ta'addanci

An gano asalin mutumin da ake zargin dan ta'adda ne wanda aka kashe shi a Brussels a lokacin wani samani a ranar Talata.

Mutumin mai suna Mohammed Belkaid, dan kasar Algeria ne kuma bai da cikakkun takardun zama a kasar Belgium.

Hukumomi sun ce an kashe shi ne a lokacin da ya bude wuta kan 'yan sanda a gidansa da ke wata unguwa da ake kira Forest a wajen birnin Brussels.

Kawo yanzu 'yan sanda na ci gaba da farautar wasu mutane biyu da ke cikin gidan a lokacin da lamarin ya auku.

Samamen na cikin binciken da ake yi kan harin da aka kai a Paris, lamarin da ya janyo mutuwar mutane akalla 130 a watan Nuwamban bara.