Mutane 22 sun rasu a harin Masallaci a Maiduguri

Wasu 'yan kunar bakin wake da ake zaton 'yan Boko Haram ne sun kashe mutane akalla 22, yayin da suke Sallar asuba a wani Masallaci da ke yankin Umarari a kusa da birnin Maiduguri.

Limamin Masallacin, Malam Gwani Kyari ya shaida wa BBC cewa bam din farko ya tashi ne tun kafin su yi raka'ar farko a lokacin Sallar.

"Bam din farko ya ta shi ne kafin mu yi raka'ar farko, sannan na biyu ya tashi a wajen masallacin," in ji Liman Gwani.

Na'urarku na da matsalar sauraren sauti
Ga rahoton da Raliya Zubairu

Shi ma kakakin rundunar sojin Najeriya, Kanar Sani Usman Kukasheka a cikin wata sanarwa ya ce mata 'yan kunar bakin wake ne suka kai harin a masallacin da ke yankin Umurari a kusa da Molai da ke Maiduguri.

Rundunar sojin ta tabbatar da mutuwar mutane 22 sakamakon harin, a yayin da wasu fiye da 18 suka samu raunuka.

A cewar sojin, an tura karin dakaru zuwa yankin domin bayar da kariya.