An wuce da Hama Amadou asibiti a Faransa

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Hama Amadou na daga cikin 'yan takarar shugabancin kasa a jamhuriyar Nijar

Gwamnatin Jamhuriyyar Nijar ta fita da dan takarar shugabancin kasar karkashin jam'iyyar adawa Hama Amadou, zuwa asibitin kasar waje domin duba lafiyarsa.

Wakilin BBC ya ce tuni aka kai Amadou babban birnin kasar Niamey daga Filinge inda ake tsare da shi.

An kai shi ne a wani jirgin sojojin Faransa, kuma daga nan aka wuce da shi Paris domin duba lafiyar tasa.

Har yanzu ba a san kowacce irin cuta ce ke damun Amadou ba.

Amadou na daga cikin 'yan takarar shugabancin kasar Nijar, amma tun a shekarar da ta gabata ne yake tsare a gidan yari saboda tuhumarsa da ake yi da safarar jarirai.

Sai dai ya musanta zargin, yana mai cewa an yi hakan ne don a hana shi takarar shugabancin kasar.

A ranar Lahadi za a sake zagaye na biyu na zaben shugaban kasa a jamhuriyyar ta Nijar.

A ranar Talata ne aka tsare likitan Hama Amadou wato Yakubu Haruna, saboda nuna damuwarsa da ya yi kan lafiyar dan takarar.

Karin bayani