NNPC ya musanta karkatar da kudi

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Najeriya ta dogara da danyen man fetur domin bunkasar tattalin arzikinta

Kamfanin man fetur na Najeriya, NNPC ya musanta zargin cewa bai saka da dala biliyan 16 ba a cikin asusun haraji na gwamnatin kasar.

Sai dai NNPC din ya ce dala biliyan daya da miliyan dari shida ne ake bin shi.

A farkon wannan makon ne, ofishin babban mai binciken kudi na gwamnati, ya yi zargin cewa a shekara ta 2014, dala biliyan 16 sun yi layar zana daga lalitar gwamnati.

A cikin wata sanarwa, NNPC ya ce wani rahoto ne da mai bincike kan harkokin kudaden Najeriya ya fitar, bai yi daidai ba saboda bai yi la'akari da kudin tallafin man fetur da kuma fasa bututan mai.

Tun lokacin da shugaba Muhammad Buhari ya hau karagar mulki a watan Mayun bara, ya yi alkawarin kawar da duk wasu ayyuka na almubazaranci da karbar hanci da ke neman durkusar da kasar.

Bisa kundin tsarin mulkin kasar dai, dole ne NNPC ya kudin da ya samu daga sayar da danyen mai, wanda zai kai kimanin kashi 70 cikin dari na dukkanin kudaden da kasar ke samu, saboda kudaden za su shiga cikin kasafin kudin da aka yi.