Obama ya zabi Garland a matsayin alkali

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Akwai yiwuwar Garland ya fuskanci adawa daga 'yan Republican

Shugaba Obama ya bayyana Merrick Garland a matsayin wanda yake so ya nada a matsayin alkali a kotun kolin kasar.

Mista Obama ya ce mai shari'a Garland, ya shirya zamowa daya daga cikin masu shari'a a kotun.

Ana kallon alkalin a matsayin mai sassaucin ra'ayi, wanda ya samu yabo daga wajen kusoshin jam'iyyar Republican.

Amma dai 'ya'yan jam'iyyar ta Republican a majalisar dattawa, sun ce ba za su goyi bayan nadin duk wanda Obama ya mika musu ba.

Nadin zai fayyace ko masu tsattsaurar ra'ayi ko kuma masu sassauci za su samu rinjaye a kotun kolin mai alkalai tara.

'Yan Republican sun fi son wanda zai ga ji Obama a zaben watan Nuwamba, ya zabi wanda zai shiga cikin sawun alkalan babbar kotun.