A shirye muke mu tattauna da Iran — Saudiya

Image caption Yarima Turki al-Faisal ya ce kasashen biyu suna da abubuwa daya da za su iya gina wa a kai

Wani babba a masarautar Saudiyya ya shaida wa BBC cewa a shirye kasarsa ta ke ta tattauna kai tsaye da abokiyar hammayarta a yankin watau Iran, muddin ta nuna cewa za ta janye dakarunta daga Syria.

Yarima Turki al-Faisal ya ce kasashen biyu suna da abubuwa daya da za su iya gina wa a kai.

Har wa yau Yariman ya yi marhabin da janyewar dakarun Rasha da yawa daga Syria, kuma ya ce duk sojojin kasashen waje su ma su fice daga kasar.

Yarima al-Faisal ya kuma yi tsokaci a kan luguden wuta da sojin kasarsa ke yi a Yemen, inda ya ce ba za a dakata da wannan aiki ba in har 'yan atwayenHouthi da Iran kegoyon baya ba su yarda da tattaunawar zaman lafiya ba.

Karin bayani