BH: Kamaru ta yanke hukuncin kisa kan mutane 89

Hakkin mallakar hoto no
Image caption Gwamnatin Kamaru na aiki kafada da kafada da Najeriya don kawo karshen ayyukan Boko Haram

Kotun soji a birnin Maroua da ke jamhuriyar Kamaru, ta zartar da hukuncin kisa a kan wasu mutane 89 da ta samesu da laifin kai hare-hare ko kuma bayar da hadin kai ga kungiyar Boko Haram.

Wadannan mutane sune kashi na farko daga cikin fursunoni 850 da suke gidan yari, wadanda ake zargi da haddasa ta'addanci.

Kungiyar Boko Haram ta yi kaurin suna a yankin tafkin Chadi, inda dumbin mutane suka rasa rayukansu sakamakon kisan gilla da kuma sanadin hare-haren kunar bakin wake.

Lamarin da ya kai ga gwamnatin Kamarun kirkiro doka ta musamman dangane da ayyukan ta'addanci.