Man U ta shiga rudani a kan zaben sabon koci - Vidic

Hakkin mallakar hoto PA
Image caption Nemanja Vidic: Tsohon dan wasan baya na kungiyar Man Utd

Tsohon dan wasan baya na kungiyar Manchester United Nemanja Vidic, ya yi amanar cewar kungiyar za ta fuskanci rudani, wajen yanke shawarar zaben wanda zai maye gurbin Louis van Gaal a matsayin koci.

Kungiyar dai na sa ran zaben sabon kocinta tsakanin Jose Mourinho da kuma Ryan Giggs.

Kwantiragin Van Gaal ba zai kare ba har sai karshen shekarar 2016, amma yana fuskantar matsin lamba tun bayan da aka bai wa kungiyar kashi a wasan kakar bana.

Giggs da Mourinho sun bayyana a sahun farko na wadanda ake sa ran za su karbi jagorancin kungiyar idan har Van Gaal ya tafi.