Na'urarku na da matsalar sauraren sauti

Izala na taron tabbatar da zaman lafiya

Hakkin mallakar hoto mosque website
Image caption Taron na wanzar da zaman lafiya ne tsakanin al'uma.

A Najeriya an bude wani babban taron musulunci da kungiyar Izalatul Bidi'a wa Iqamatul Sunna ta shirya da hadin gwiwar kungiyar musulmi ta duniya da ke da cibiya a Saudi Arabia.

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari, da wasu gwamnoni, da kuma sarakunan gargajiya sun halarci wajen bude taron.

Wadanda suka shirya taron dai sun ce, manufarsa ita ce, duba batutuwan samar da zaman lafiya da kuma hada kan musulmi.

Kamar yadda Sheikh Abdullahi Bala Lai shugaban kungiyar Izala ta kasa ya shaidawa BBC.