'Kungiyar IS ta aikata kisan kare dangi'

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Dubban mutane sun mutu a rikicin Syria

Sakataren wajen harkokin wajen Amurka, John Kerry, ya zargi kungiyar IS da aikata laifukan kisan kare dangi a kan masu addini 'yan tsiraru a gabashin Afirka.

A lokacin da ya ke gabatar wani jawabi a Amurka, Mista Kerry ya ce kungiyar IS ta kai hare-hare kan masu addinin Yazidi da kiristoci da kuma 'yan Shi'a.

Wannan ne karo na biyu da gwamnatin Amurka ta yi furucin cewa an yi kisan kare dangi a rikicin Syria.

Jawabin ya bukaci Amurkar ta hukunta duk wani mai hannu a kisan.

Sai dai wakilin BBC a Amurka, ya ce babu tabbas a kan yadda wannan zai sauya manufar Amurka a kan rikicin na Syria.