Majalisa ta kada kuri'ar goyon bayan Ganduje

Image caption Gwamnan Kano: Abdullahi Umar Ganduje

Majalisar dokokin jihar Kano da ke arewacin Najeriya ta kada kuri'ar goyon baya ga gwamna Abdullahi Ganduje a matsayinsa na jagoran jam'iyyar, a maimakon tsohon gwamna Rabiu Musa Kwankwaso.

Haka kuma an tsige gagarabadau na majalisar, wanda ya kasance mai goyon bayan Sanata Kwankwaso, kuma tuni aka maye gurbinsa da wani dan majalisar mai goyon Ganduje.

A baya bayan nan wasu 'yan majalisar sun kai ziyara fadar gwamantin jihar Kano inda suka yanke shawarar ajiye jajajayen hulunansu, wanda ita ce alamar kwankwasiya wanda tsohon gwamnan, Rabiu Musa Kwankwaso ke jagoranta, a yayin da gwaman Kanon, Abdullahi Umar Ganduje ya rarashesu su si cigaba da sakawa.

'Yan majalisar sun yi alkawarin ba za su sake sanya jajayen hulunan ba, wadanda duk wani dan jam'iyyar APC a jihar Kano ke sawa tun zamanin mulkin Kwankwaso a shekarar 2011 don nuna mubaya'arsu gare shi.