An ware Naira biliyan 10 don matasa

Dalibai masu bautar kasa a Nigeria Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Rashin aikin yi babban kalubale ne ga matasa.

A Najeriya gwamnatin shugaba Muhammadu Buhari ta kaddamar da wani shiri na samar da ayyukan yi ga matasa.

Shirin wanda Bankin masana'antu ya kaddamar ya ware Naira Biliyan 10 domin ba wa matasa bashi don dogaro da kai.

Ministan Kasuwanci da sanya jari Okechukwu Enelamah ya ce ma'aikatar sa za ta hada gwiwa da wasu cibiyoyi na gwamnati domin shirin ya samu nasara.

Rashin aikin yi na daya daga cikin matsalolin da matasa suke fuskanta a Najeriya ko da kuwa sun yi ilimi mai zurfi.

Harwayau, an dangata rashin aiki na sanya matasa shiga kungiyoyin masu aikata muggan laifuka da sauran su.