'Yan adawa sun gamsu da kai Hama asibiti

Hama Amadou. Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption 'Yan adawa a jamhuriyar Nijar sun ce gwamnati da kan ta ta gano Hama ya na bukatar kulawar likita.

Jam'iyar Moden Lumana ta Hama Amadu ta nuna gamsuwarta game da matakin da gwamnatin jamhuriyar Nijar ta dauka na kai jagoran 'yan adawan kasar Faransa domin a yi masa magani.

Jam'iyar ta ce ba ta da wani shakku dangane da asibiti da kuma likitocin da za su kula da Hama Amadun.

A ranar Laraba ne dai wani jirgin Faransa ya dauki Hama Amadun, wanda ke takara a zaben shugaban kasar zagaye na biyu da za a yi ranar Lahadi, zuwa Paris.

Kakakin jam'iyyar Alhaji Mahaman Lawali Salisu, ya shaidawa BBC cewa binciken da likitan Hama Amadou ya gabatar, da binciken da bangaren gwamnati suka yi ya zo daya, don haka ne ma gwamnati ta amince a fitar da shi zuwa asibiti a Faransa don yi masa magani.

Tun a watan Nuwambar bara ne ake tsare da Hama Amadou a gidan kaso, bisa zargin da ake ma sa cewa yana da hannu a badakalar sayo jarirai daga Najeriya.

Hama dai ya musanta wannan zargi, ya na cewa bita da kullin siyasa akai ma sa.