Koriya ta arewa ta sake tsokanar fada

Makami mai linzami Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Tun a farkon wannan shekarar Koriya ta arewa ta fara harba makamai masu linzami.

Amurka ta ce kasar Koriya ta arewa ta sake harba wani makami mai linzami har sau biyu cikin tekun da ke gabashin kasar, bayan 'yan kwanaki da umurnin da shugaban kasar Kim Jong-un ya bayar cewar a ci gaba da jarraba makaman nukiliya da masu linzami.

Amurka dai ta mai da martani ne tana gargadin Koriya ta arewa da ta guji jefa yankin cikin zulumi.

Kamfanin dillancin labaran Koriya ta kudu ya ce makami mai linzami na biyu da Koriya ta arewar ta harba ya tarwatse a sararin samaniya.

Wata majiyar sojin Koriya ta kudu ta ce an yi amfani ne da makami mai linzami na Rodong, wanda ke tafiyar kilomita 1300.

An dai fara zaman dar-dar a kan iyakar Koriya ta kudu, tun lokacin da makwabciyarta Koriya ta arewa ta jarraba wani makamin nukiliya a watan Janairun da ya wuce.