Za mu ci gaba da goyon bayan Assad - Putin

Hakkin mallakar hoto RIA Novosti
Image caption Assad na samun goyon bayan Putin

Shugaba Vladimir Putin na Rasha ya ce gwamnatinsa za ta ci gaba da taimaka wa gwamnatin Syria, kuma a shirye ta ke ma, ta kafa sansanin sojinta a yankin cikin 'yan sa'o'i in bukatar hakan ta taso.

A jawabin da ya yi wa sojojin Rashan da suka koma gida daga Syria, shugaba Putin din ya ce sojojin sun yi bajinta a yaki da ta'addanci, sannan, sun bude kofar samun zaman lafiya.

Mista Putin ya ce shugaba Bashar Al-Assad na Syrian ya yi na'am da matakin da Rashan ta dauka na janye wasu dakarunta daga kasar.

Ya kuma ce Moscow, ba za ta kyale ko wacce kasa cin karenta ba babbaka a sararin samaniyar Syrian ba.