An kashe mayakan Al shabab 30

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Mayakan Al shabab na yawan kai hare-hare Somaliya

Shugabannin dakarun gwamnatin Somaliya da Kenya, wadanda aka girke a Somaliyar sun ce sun kashe mutum 30 da suke zargin cewa mayakan kungiyar Al shabab ne.

Shugabannin sojojin wadanda ke lardin Puntland, sun kashe mayakan Alshabab 11 lokacin da suka yi yunkurin kwace iko da wasu kauyuka da ke bakin ruwa.

A bangare guda kuma Sojojin Kenya sun ce sun kashe mayakan Al shabab 19, wadanda suka kai hari kan sansanin soji da ke birnin Afmadhow, wanda ke kudancin Somaliyar.