Ba wanda ke nuna isa a kaina - Zuma

Hakkin mallakar hoto
Image caption Shugaba Zuma ya ce ba wani mai karfin iko a kansa da tsarin mulkinsa

Shugaban kasar Afirka ta Kudu, Jacob Zuma, ya musanta zargin da ake masa cewa iyalan wani babban gida da ke da fada aji a kasar, suna nuna isa a kansa, wajen zaben mutanen da ake nadawa ministoci.

Mista Zuma ya ce shi kadai ne yake zaban mutanen da yake basu mukamai a gwamnatinsa.

A ranar Laraba ne wani babban dan siyasa a kasar, Mcebisi Jonas, ya ce iyalan gidan Gupta, sun masa tayin mukamin ministan kudi na kasar.

Sai dai iyalan gidan na Gupta, sun musanta wannan zargi.

Shugaba Zuma ya sha tambayoyi masu zafi lokacin da ya bayyana a gaban majalisar dokokin kasar, a kan zargin da ake na cewa iyalan gidan na Gupta suna nuna isa a kansa.

Jagoran 'yan adawa a Majalisar, Mmusi Maimane, ya bukaci shugaba Zuman da yayi murabus saboda zargin.

Ya ce, "Tambaya ta gare ka shugaba Zuma ita ce ko iyalan gidan Gupta sun taba yi ma wani tayin mukami a majalisarka, ko kuma Mista Jonas karya ya yi mana."

Karin bayani