Amurka za ta ninkawa Koriya takunkumi

Kim Jung-un Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Ba wannan ne karon farko da ake ninkawa Koriya ta Arewa takunkumi ba.

Shugaban Amurka, Barak Obama ya rattaba hannu a kan wani sabon takunkumi da za a kakaba wa kasar Koriya ta arewa sakamakon gwajin makamin nukiliya da wasu makamai masu linzamin da ta yi.

Kakakin Fadar White House ta shugaban Amurkan ya ce Amurka da sauran kasashen duniya ba za su saurara wa abubuwan da Koriyar ta arewar ke yi da makamin nukiliya ba.

Tun da farko dai Amurkan ta zargi Koriya ta Arewar da kokarin rabewa da guzuma domin ta harbi karsana ta hanyar gallaza wa wasu Amurkawa domin cimma wani burinta na siyasa, bayan Koriya ta arewar ta yanke wa wani dalibi Ba'amurke hukuncin daurin shekara 15 a gidan yari da kuma horo mai tsanani bayan ta kama shi da satar wani kyallen siyasa a wani Otel.