FBI ta yi gargadi akan barazanar kutse a motoci

Hakkin mallakar hoto fbi
Image caption An shawarci jama'a da su tuntubi FBI kan kutse a motocin su

Hukumar binciken manyan laifuka ta Amurka FBI tare da hukumar kiyaye hadurra a manyan hanyoyin kasar sun yi tsokaci game da ci gaba da nuna damu wa da ake yi kan barazanar kutse a motoci.

A wata takardar shawara da suka fitar, hukumomin sun gargadi jama'a da su yi la'akari da barazanar tsaro da ake fuskanta game da tsaron motoci.

A bara kamfanin kera motoci na Fiat Chrysler ya janye wa su motoci miliyan 1 da dubu dari 400 a Amurka bayan da masu bincike kan sha'anin tsaro suka yi amfani da na'ura wajen sarrafa motoci kirar Jeep daga waje.

An dai shawarci jama'a da ke zargin an yi kutse a motocin su da su gagggata tuntubar hukumar binciken manyan laifuka ta Amurka wato FBI.