Ana sasanta Kwankwaso da Ganduje

Hakkin mallakar hoto Halilu Dantiye
Image caption Ana kokarin sasanta Kwankwaso da Ganduje

Gwamnan Kano Abdullahi Umar Ganduje yace zai sasanta sabanin da ke tsakaninsa da tsohon gwamnan jihar Sanata Rabiu Musa Kwankwaso

Ganduje ya baiyana haka ne ga yan jarida bayan da ya gana da shugaba Muhammadu Buhari a fadar gwamnati a Abuja.

Gwamnan yace sabanin da ya taso tsakaninsa da Sanata Kwankwaso matsala ce ta cikin gida kuma sun shawo kan al'amarin.

Ya baiyana dangantakarsa da Kwankwaso da cewa tamkar yan uwa suke kuma abokai a siyasance, yana mai cewa ba za su bari sabanin ya bata zumuncinsu ba.

Bayanai sun ce akwai yunkuri da ake yi a matakai da dama na ganin an dai-dai ta tsakanin bangarorin biyu ya yi nisa, kuma har ana fatan kwalliya zata biya kudin sabulu.

Bangarori da dama a ciki da wajen jihar Kano sun damu da rikicin da ya barke tsakanin gwamna Ganduje da Sanata Kwankwaso, mutanen da aka sansu da aminci na siyasa shekaru da dama.