MTN ya janye karar da ya shigar

Hakkin mallakar hoto

Kamfanin sadarwa na MTN ya ce ya janye karar da ya shigar tsakaninsa da gwamnatin Najeriya.

A cewar kamfanin, yin hakan zai bayar da damar cigaba da tattaunawa a kan yadda zai sasanta da hukumomin Najeriiya a kan yadda za a shawo kan lamarin domin taimakon kansa da kuma Najeriya.

A ranar 24 ga watan Fabrairun shekarar 2016 ne, kamfanin MTN ya sanar da janye karar da ya shigar kuma ya biya dala biliyan 50 ba tare da gindaya wani sharadi ba.

Ya biya wadannan kudade ne a kan cewar za a yi amfani da su wajen yin masalaha idan har an kai ga hakan.

A cewar shugaban MTN na Najeriya, "mun cika alkawarinmu na janye karar da muka shigar kuma mun tabbatar da hakan ta janyewa a hukumance.Wannan na daga cikin matakanmu na tabbatar da zaman lafiya a matsayinmu na masu kasuwanci mazauna kasa."

Janye karar da MTN ya shigar a babban kotun tarayya, wanda ya samu hallartar bangarorin biyu, alama ce da ke nuna samun cigaba a yarjejeniya tsakanin MTN na Najeriya da kuma hukumomin kasar.