Mahawara kan zagaye na biyu a zaben Nijar

Image caption Jagororin yakin neman zaben jam'iyyun da ke takara a jamhuriyar Nijar.

'Yan takara, Shugaba Mahamadou Issoufou da kuma jagoran 'yan adawa Hama Amadou, sun samu kashi 48.43 cikin dari da kuma kashi 17.73 kowannensu a zagayen farko.

Mataimakin jagoran da ke gudanar da yakin neman zaben jam'iyyun hamayya, watau Copa 2016, Moussa Haro, ne ya kara da Assoumana Malam Issa, wanda shi ke da alhakin hada kan ayyukan yakin neman zaben shugaba Mahamadou Issoufou.

Sama da mutane miliyan 7 ne ake kyautata zaton za su yi zabe, a rana 20 ga watan Maris, ganin yadda aka wuce da Hama Amadou asibiti birnin Paris saboda duba lafiyar sa.

Tun a watan Nuwambar da ta gabata ne, Hama Amadou ke tsare gidan kaso, saboda zargin sa da laifin safarar kananan yara.

Jam'iyyar adawa dai ta ce za ta kauracewa zaben, inda kuma take cewa bata yarda da yadda aka gudanar da zaben a zagayen farko ba, inda ta ke zargin an yi coge a yayin da dan takarar su ke tsare.

Kazalika jam'iyyar adawar ta nuna damuwa game da lafiyar dan takararta.

Moussa Haro, ya ce an zubar wa Hama Amadou da mutuncinsa.

Amma kuma Assoumana Malam Issa ya ce "An samu ci kwanciyar hankali a Nijar", idan aka duba kalubalen tsaro da ta shiga.

Ba a san maci tuwo ba, sai miya ta kare, a ranar Lahadi za a yi zaben.