BH: An kashe jami'an tsaro a Niger

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption An sha kai hare-hare Nijar

Wasu 'yan sanda guda uku da soja daya sun rasa rayukansu a wasu hare-hare da aka kai a jamhuriyar Nijar.

Al'amarin ya faru ne a ranar Alhamis, kwanaki uku gabanin zagaye na biyu na zaben shugaban kasa da za a gudanar.

Kamfanin dillancin labarai na AFP ya ruwaito cewar ana zargin wasu 'yan kungiyar Al-Qaeda ne suka harbe 'yan sandan a wata kasuwa da ke Dolbel kusa da kan iyakar Burkina Faso.

Daya harin kuwa wasu 'yan kunar bakin wake hudu ne suka kai kan jerin gwanon motocin soji kusa da iyakar Najeriya, inda suka kashe soja daya tare da ji wa wasu biyun rauni.

Kazalika, jami'ai sun ce sun samu nasarar dakatar da wata yarinya tayar da nata bam din da ke daure a jikinta.

A baya dai Nijar ta sha fuskantar hare-hare daga kungiyar Boko Haram mai cibiya a Najeriya.