Sarakuna biyar masu mulkin kama karya

Fadar Nicolae Ceausescu mai suna "Spring Palace" a Bucharest da ke kasar Romania
Image caption Gidan Nicolae Ceausescu’s wanda za a sake budewa jama'a a karo na farko, shekaru 27 bayan rushewar mulkin kwamanasinci a kasar Romania.

A matsayinsa na fadar da gwamnatin kasar ta bai wa iyalan Ceausescu a garin Bucharest, za a bude wa al'umma kofofin fadar a ranar 19 ga watan Maris, kuma BBC na bibiyar wannan da sauran fadar zaman wasu tsofaffin shugabannin da suka yi mulkin mallaka.

An budewa al'umma fadar tsoffin iyalan da suka shugabanci kasar Romania, bayan fiye da shekaru 25 da suka yi a rufe bayan faduwar tsarin kwaminisanci.

Nicolae da Elena Ceausescu sun zauna a fadar da ke babban birnin kasar watau Bucharest, a shekarun 1960, lokacin da yawancin 'yan Romania ke cikin matsanancin talauci.

An yi masu korar kare sannan kuma aka sa sojoji suka harbe su a shekarar 1989.

Duk da sunan fada da aka sanya mata, ginin dan karamin gida ne mai fili sosai, inda aka yi masa fenti da kalolin zinari, ga kujeru da gadaje da aka yi da kwakkwarar katakai masu nauyi, da kwalliya bango da kaloli daban-daban.

Yanzu dai baki za su iya zagayawa duk dakuna 80 din da ke fadar, har ma da dakin kallon sinima, da wurin ninkaya watau swimming pool, da dakin kwalliya-wanda aka gine a filin kimanin mita 14,000 a unguwar masu halin da ake cewa Primaverii da ke Bucharest.

Bayan boren da aka gudanar na shekarar 1989 a Bucharest ne ginin ya koma hannun gwamnatin kasar, inda kuma ba kasafai ake amfani da shi ba sai dai domin sauke manyan baki.

An sanya shi ma a kasuwa a shekarar 2014, amma bai yi farin jini ba.

Fadar Muammar Gaddafi mai suna Bab Al-Aziziya da ke Tripoli a kasar Libya
Image caption 'Yan tawayen Libya, inda suke kwasar garabasa daga cikin fadar Bab al-Aziziya gabannin kwace gidan a shekarar 2011.

Fadar Bab al-Aziziya ta kasance muhallin shugaban Libya Muammar har lokacin da 'yan tawaye suka kama shi a shekarar 2011, lokacin da aka yi yakin basasar kasar.

An lullube fadar cikin sirri da tsaro a lokacin da Kanar Gaddafi ya zauna, inda 'yan Libya ke tsoron tunkarar ciki.

Fadar wata manuniya ce ga yadda ake kallon mulkin Kanar Gaddafi, inda 'yan tawaye suka kwace fadar bayan wani hari da suka kai babban birnin kasar a watan Agustan wannan shekarar.

An nuno hotunan yadda 'yan tawaye suka fasa kawunan mutum-mutumin da aka gina da siffar Gaddafi, suna kwallo da shi a cikin fadar.

An gano boyayyun hanyoyi cikin fadar, kazalika rahotanni sun nuna cewa akwai dakin tiyata har ma da dakunan asibiti, da filin buga kwallon gulf duk a boyayyun hanyoyin da ke cikin fadar.

A watan Oktoban wannan shekarar ne, manyan motocin rushe gine-gine suka fara rusa bangon fadar, amma basu ida rushe shi har kasa ba.

An dai bayar da shawarar cewa a karasa rushe fadar, domin a gina sabon wajen shakatawa a filin.

Fadar Ferdinand da Imelda Marcos mai suna Santo Nino shrine, da ke Tacloban a kasar Philippines
Image caption An gina fadar Santo Nino Shrine garin Imelda Marcos, wanda ke Tacloban.

An soma gina wannan katafaren gida a shekarun 1970, aka kammala shi a shekarar 1981- a lokacin da mulkin Ferdinand Marcos na shekaru ashirin suke kawowa karshe.

An gina fadar ce a Tacloban, garin mai dakinsa Imelda, kuma aka masa lakabi da sunan wani malamin addini, kazalika ma'adani ga tarin zane da tangaran, har ma da tulun fure da aka yi wa zane-zanen da a saba gani ba, da kuma hauren giwa da shi ma aka yi wa zane, da dai sauran abubuwa da ke nuna irin almubazarancin da aka shafe shekaru ana yi a wannan mulkin.

Ginin na kimanin mita 21,500, yana da wani babban daki da wajen wanka mai fadi na 'yan wasan Olympics, da dakunan cin abinci, da dakunan baki 13, kowanne dauke da zane-zanen bango da ke nuna yankunan kasar.

Fadar na daya daga cikin akalla gidajen shakatawa 29 mallakin shugaban da ke watse a kasar.

Yanzu dai an mayar da shi gidan adana tarihi.

An kashe Ferdinand Marcos a shekarar 1986, a wani bore da 'yan kasar suka gudanar da goyon bayan sojoji bayan ya shekarar 20 yana mulki.

Fadar Viktor Yanukovyh mai suna Mezhyhirya da ke birnin Kiev a kasar Ukraine
Image caption An bude fadar tsohon shugaban Ukraine Viktor Yanukovych mai suna Mezhyhirya ga al'umma bayan ya tsere daga kasar. Ukraine

An bude kofofin wannan shahararren gini na tsohon shugaban Ukraine Viktor Yanukovych, bayan majalisar dokokin kasar ta gudanar da zabe, kan a tumbuke shi daga mulki a watan Fabrairun shekarar 2014, daga bisani kuma fadar Mezhyirya ta koma hannun gwamnati.

Shugaban dai ya samu mafaka a Rasha.

A cikin fadar da aka sani da Mezhyhira, wanda ke wajen Kiev, babban birnin kasar, akwai kasaitattun gine-ginen da aka zageye da lambu.

Cikin fadar ma akwai gidan ajiye dabbobi, da wajen wucewar ruwa da aka gina na sha'awa, har da filin buga kwallon golf.

An kuma kawata lambunan fadar da gine-ginen mutum-mutumi da kananan rafi da filayen buga wasan tennis.

Wannan tsarin, ga yawancin masu zanga-zangar adawa da gwamnati, ya nuna almubazaranci da almundahanan da mulkin ya kunsa.

Fadar Saddam Hussein da ke birnin Bagadaza a kasar Iraki
Image caption Yawancin al'ummar Iraki na zama cikin matsanancin hali na yunwa, amma shi Saddam Hussein na zama cikin wadata a kasaitattun gidaje na gani na fada a duniya.

A shekarar 2003, wata hadakar sojojin da Amurka ta jagoranta suka shiga kasar Iraki domin hambarar da Saddam Hussein daga mulki.

A karshen wannan shekarar ne aka kama Saddam Hussein, sannan a shekarar 2006 aka yanke masa hukuncin kisa, ta hanyar rataya.

Saddam Hussein na da fada daban-daban watse a cikin birnin da ma kasar baki daya, inda daya cikin su ke da cibiyar gudanar da harkokin tsaro daga karkashin kasa, da kuma wajen samar da makamashin nukiliya.

Akwai kuma wata tashar samar da wutar lantarki da wajen tace iska da ruwan sha.

Akwai wata fada a Basra da ke kudancin Iraki, da Saddam ya gina a shekarar 1990, wanda ke da tagogi 56, da manyan dakuna 18 da zauren shan iska 12 da dakuna ba haya 8 da matakala biyar da kuma kebebben dakuna daga saman rufi guda uku.

Wannan na daya kenan daga cikin katafare da kuma kasaitattun gine-ginen da ke cikin fadar.