An dakatar da shugaban jam'iyyar APC a Kano

Image caption An dakatar da shugaban jam'iyyar APC da sakataren tsare-tsare a Kano

Jam'iyyar APC a Kano tace ta dakatar da shugaban ta na jihar da kuma sakataren tsare-tsare bisa zargin su da yin gaban kan su a wasu ala'mura da suka shafi jam'iyyar.

Haka kuma jam'iyyar ta kafa wani kwamitin ladabtarwa da zai duba zargin da ake yiwa mutanen da aka dakatar, ya kuma bada shawarar matakin da ya kamata a dauka.

To sai dai mutanen da aka dakatar da su sun yi watsi da matakin uwar jam'iyyar ta su.

A wajen wani taro ne dai da 'ya 'yan jam'iyyar musamman masu rike da mukamai da aka zaba da kuma shugabannin mulki na jam'iyyar suka gudanar aka bayyana matakin dakatar da shugaban jam'iyyar Alhaji Umar Haruna Doguwa, da kuma sakataren tsare tsare na jam'iyyar Alhaji Sunusi Surajo Kwankwaso bisa zargin yin wasu abubuwa da suka shafi jam'iyyar ba tare da sahhalewar jam'iyyar ba.

Matakin na jam'iyyar dai ya zo ne a dai-dai lokacin da ake yunkurin sulhu tsakanin Gwamna Abdullahi Ganduje na jihar Kano da kuma Sanata Rabiu Musa Kwankwaso wanda wasu ke ganin matakin jam'iyyar tamkar kara rura wutar rikicin ne.

Tuni dai wadan da aka ce an dakatar daga jam'iyyar wadan da an san su tsantsar 'yan kwankwasiyya ne suka yi watsi da matakin da aka dauka a kan su.