Ganduje: Kwankwaso Dan uwana ne

Hakkin mallakar hoto Halilu Dantiye

Gwamnan Kano Abdullahi Umar Ganduje yace zai sasanta sabanin da ke tsakaninsa da tsohon gwamnan jihar Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, hasali ma dai yace kokarin cimma wannan yunkuri ya yi nisa.

Ganduje ya baiyana haka ne ga yan jarida bayan da ya gana da shugaba Muhammadu Buhari a fadar gwamnati a Abuja.

Gwamnan yace sabanin da ya taso tsakaninsa da Sanata Kwankwaso matsala ce ta cikin gida kuma sun shawo kan al'amarin.

Ya baiyana dangantakarsa da Kwankwaso da cewa tamkar yan uwa suke kuma abokai a siyasance, yana mai cewa ba za su bari sabanin ya bata zumuncinsu ba.