Najeriya ta ware kudi don bincike a jami'o'i

Hakkin mallakar hoto State House
Image caption Gwamnatin Najeriya ta ce kudaden za su taimaka ta fuskar bincike a fannonin kiwon lafiya da sauran su.

Gwamnatin Najeriya ta ce za ta samar da talafin Naira biliyan uku ga jami'o'in gwamnati domin gudanar da bincike da za su kawo ci gaban kasa.

Shugaban hukumar kula da jami'oi ta kasar Farfesa Julius Okojie shi ne ya sanar da haka a bikin cikar jami'ar Usman Danfodio da ke Sokoto shekaru arba'in da kafuwa da aka gudanar ranar Asabar.

Malam Ibrahim Yakasai shi ne kakakin hukumar ya kuma shaida wa BBC cewa za'a yi amfani da kudaden ne don karfafa guiwar malaman jami'o'i wajen ci gaba da gudanar da bincike a fannonin dabam dabam.

Ya kara da cewa kudaden za su taimaka sosai ta fuskar bincike a fannonin kiwon lafiya da zamantakewa da sauran su.