Nigeria: Ana zabe cikin dar-dar a Rivers

Image caption Rumfar zabe a Najeriya

Rahotanni daga jihar Ribas na cewa an yi tashin hankali a wasu mazabu a zaben da ake yi a yau na cike gurbin majalisun dokokin jihar da kuma na tarayya.

A hirar da BBC ta yi da Nick Dazang kakakin hukumar zaben ta kasar ya ce, an samu jinkirin soma zabe a wasu mazabu a karamar hukumar Bonny da Elemi a inda aka yi ta harbe-harben bindiga a daren jiya zuwa wayewar gari.

A wata hirar ta BBC da kakakin rundunar 'yan sandar jihar DSP Mohammed, ya ce rundunar ta dauki dukkanin matakan tsaron da ya kamata na ganin an yi zabe lafiya.

Sai dai rahotanin na cewa an yi rikici a Alesa da Olode inda aka yi harbe-harbe aka kuma kona wata motar bas.

A Akuku Toro kuwa, ana zaman dar-dar saboda zargin cewa an kai takardar sakamakon zabe na bogi a mazabar, hukumar zabe ta INEC ta karyata zargin a wata sanarwa da ta sa a intanet, ta kuma yi kira ga jama'a da su fito su yi zabe.