An kai harin bam a Istanbul

Hakkin mallakar hoto EPA
Image caption 'yan sanda sun killace wurin da bam din ya tashi a layin Istiklal inda ake gudanar da kasuwanci a birnin Santanbul

Bam ya tashi a tsakiyar yankin da ake gudanar da kasuwanci a birnin Santanbul na Turkiyya.

Kafofin yada labarai na kasar na cewa mutane hudu sun hallaka akalla ashirin kuma sun jikkata a harin da ake zargin na kunar bakin wake ne.

Wasu hotunan da gidan talbijin din kasar ya watsa, ya nuna motocin daukar marasa lafiya sun garzaya zuwa wurin da Bam din ya tashi wanda 'yan sanda suka killace.

A ranar Lahadin da ya wuce ne aka kai wani harin Bam din a Ankara babban birnin kasar a inda ya hallaka mutane 37.