Sabbin matakan tsaro a Bankin Ingila

Ofishin Cibiyar ta NCSC zai kasance ne a birnin London.

Asalin hoton, PA

Bayanan hoto,

Ofishin Cibiyar ta NCSC zai kasance ne a birnin London.

Gwamnatin Burtaniya ta ce daya daga cikin muhimman abubuwan da cibiyar samar da tsaro ta cybersecurity za ta maida hankali akai shine aikin samar da tsaro a Bankin Ingila.

Ayyukan sun kun shi samar da ingantattun tsare tsare na aiki a cibiyoyin hada hadar kudade ta fuskar tunkarar kalubale da kuma barazanar da ake fuskanta daga masu kutse a Internet wanda ka iya janyo cikas ga tattalin arzikin Burtaniya.

A shekarar da ta gabata ne aka sanar da cibiyar da aka sake mata suna zuwa National Cyber Security Centre wato NCSC.

Ofishin Cibiyar ta NCSC zai kasance ne a birnin London kuma ana saran cibiyar za ta fara aiki ne gadan gadan a watan Oktoba mai zuwa.