Obama ya sauka a Havana

Image caption Obama da iyalansa sun sauka a Cuba

Shugaba Obama ya fara ziyarar sa mai cike da tarihi zuwa Havana inda zai kasance shugaba na farko da zai saka kafarsa a kasar Cuba a cikin shekaru tamanin da takwas.

Shi da iyalansa sun sauka a kasar inda ministan harkokin wajen kasar ta Cuba Bruno Rodriguez ya tarbe su.

Shugaba Obama zai gana da shugaban kasar ta Cuba Raul Castro a ranar litinin inda ake kyautata tsammanin za su tattauna a kan batun cinikayya da kuma harkokin siyasar kasar.

Tuni dai gwamnatin Cuba ta ce a shirye take ta tattauna a kan kowane batu a ziyara mai tarihi da shugaba Obama ya kai.