An tasa keyar Ntaganzwa zuwa Rwanda

An tasa keyawar wani babban wanda ake zargi da kisan kare dangi a Rwanda daga Jamhuriyar Dimokradiyyar Congo zuwa kasar ta Rwanda inda zai fuskanci shari'a.

An zargi Ladisla Ntaganzwa da shirya kisan da kuma cin zarafin dubban yan kabilar Tutsi a shekarar 1994.

An kama shi a bara a Jamhuriyar Dimokradiyyar Congo.

Amurka wadda ta sanya tukwicin dala miliyan biyar a kansa ta baiyana shi a matsayin daya daga cikin wadanda suka tunzura kisan kare dangi a kudancin gundumar Butare.

An kashe dubban mutane a Rwanda a shekarar 1994 galibinsu yan Tutsi.